Southampton na bukatar sabon koci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester United ta tattaunawa da St Mary kan batun sayan Luke Shaw mai shekaru 18 akan kudi fam miliyan 27

kungiyar Southampton ta ce ba ta da wani shiri na yin cinikin wani dan wasa a halin yanzu har sai ta nada sabon koci.

Southampton dai ta sayar wa Liverpool dan wasan gabanta Rickie Lambert mai shekaru 32, kan kudi fam miliyan hudu a kasa da mako guda bayan da kocinta Mauricio Pochettino ya aji ye aiki inda ya koma Tottenham a matsayin koci.

Adam Lallana da Luke Shaw su ne dai aka yi batun cinikinsu a kwanakin baya.

Cikin wata sanarwa da kulob din ya fitar, ya bayyana cewa, ya yanke shawarar daina cinikin 'yan wasa har sai ya nada sabon koci.

Liverpool ta sayi dan wasan tsakiya Lallana mai shekaru 26, a kuma makon da ya gabata ta fara zawarcin kyaftin din Southampton kan fam miliyan 25 haka kuma tana da muradin dan wasan bayan Croatia Dejan Lovren mai shekaru 24.