Rukunin B

Rukunin B:

Spain:

Hakkin mallakar hoto AFP

Spain za ta nemi kare kofin da ta lashe gasar da aka buga a Afrika ta Kudu a shekara ta 2010.

Kocin tawagar Vicente Del Bosque mai buga salon wasa 4-3-3 na kokarin zama koci na farko a tarihin gasar cin kofin duniya da zai lashe gasar kofin duniya sau biyu a jere.

'Yan wasan Spain da za a sa'ido a kansu sun hada da Diego Costa wanda ya zabi Spain a maimakon kasar sa ta haihuwa Brazil, da kuma sauran 'yan wasan da ke taka leda Barcelona da Real Madrid.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Iker Casillas (Real Madrid), Pepe Reina (Napoli), David De Gea (Manchester United).

'Yan wasan baya: Sergio Ramos (Real Madrid), Gerard Pique (Barcelona), Raul Albiol (Napoli), Cesar Azpilicueta (Chelsea), Juanfran (Atletico Madrid), Jordi Alba (Barcelona).

'Yan wasan tsakiya: Xavi (Barcelona), Xabi Alonso (Real Madrid), Sergio Busquets (Barcelona), Andres Iniesta (Barcelona), Cesc Fabregas (Barcelona), Santi Cazorla (Arsenal), Koke (Atletico Madrid), Javi Martinez (Bayern Munich).

'Yan wasan gaba: David Silva (Manchester City), Diego Costa (Atletico Madrid), Fernando Torres (Chelsea), Pedro (Barcelona), Juan Mata (Manchester United), David Villa (Atletico Madrid).

Netherlands:

Hakkin mallakar hoto AFP

Kasar Netherlands ba ta taba lashe gasar cin kofin kwallon duniya ba, kuma a gasar da aka buga a 2010, kasar ce ta zama ta kyautar azurfa.

Kocin tawagar wanda zai koma Manchester United a kakar wasa mai zuwa watau Louis van Gaal zai yi kokarin kafa tarihin daga kofin tare da kasar sa ta haihuwa inda zai yi fatar Arjen Robben da Robin van Persie su haskaka a gasar.

A kan hanyarta na zuwa Brazil, Netherlands ta samu nasara a wasanni 10 inda ta zura kwallaye 34.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Jasper Cillessen (Ajax), Tim Krul (Newcastle), Michel Vorm (Swansea)

'Yan wasan baya: Daley Blind, Joel Veltman (both Ajax), Stefan de Vrij, Daryl Janmaat, Terence Kongolo, Bruno Martins Indi, (all Feyenoord), Paul Verhaegh (FC Augsburg), Ron Vlaar (Aston Villa).

'Yan wasan tsakiya: Jordy Clasie (Feyenoord), Jonathan de Guzman (Swansea), Nigel de Jong (AC Milan), Leroy Fer (Norwich), Arjen Robben (Bayern Munich), Wesley Sneijder (Galatasaray), Georginio Wijnaldum (PSV Eindhoven).

'Yan wasan gaba: Memphis Depay (PSV Eindhoven), Klaas-Jan Huntelaar (Schalke 04), Dirk Kuyt (Fenerbahce), Jeremain Lens (Dynamo Kiev), Robin van Persie (Manchester United).

Chile:

Hakkin mallakar hoto AP

Kasar Chile ta tsallake zuwa wannan gasar ce bayan ta zama ta uku a tsakanin kasashen da suka fafata a nahiyar Kudancin Amurka.

Sabon kocin tawagar, Jorge Sampaoli ya bullowa kasar da wani sabon tsarin taka leda domin ganin sun samu nasara wasanninsu.

Chile za ta nemi lashe wannan gasar a karon farko a tarihinta, musamman ta yin la'akari da yadda Alexis Sanchez ke murza leda a Barcelona.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Claudio Bravo (Real Sociedad), Johnny Herrera (Universidad de Chile), Cristopher Toselli (Universidad Catolica), Paulo Garces (O'Higgins).

'Yan wasan baya: Gary Medel (Cardiff City), Gonzalo Jara (Nottingham Forest), Marcos Gonzalez (Union Espanola), Enzo Andia (Universidad Catolica), Jose Rojas (Universidad de Chile), Eugenio Mena (Santos), Mauricio Isla (Juventus).

'Yan wasan tsakiya: Jorge Valdivia (Palmeiras), Felipe Gutierrez (Twente), Rodrigo Millar (Atlas), Jose Pedro Fuenzalida (Colo Colo), Pablo Hernandez (O'Higgins), Matias Fernandez (Fiorentina), Francisco Silva (Osasuna), Arturo Vidal (Juventus), Charles Aranguiz (Internacional), Marcelo Diaz (Basel), Carlos Carmona (Atalanta), Miiko Albornoz (Malmo).

'Yan wasan gaba: Alexis Sanchez (Barcelona), Esteban Paredes (Colo Colo), Eduardo Vargas (Valencia), Gustavo Canales (Union Espanola), Jean Beausejour (Wigan Athletic), Mauricio Pinilla (Cagliari), Fabian Orellana (Celta).

Australia:

Hakkin mallakar hoto AP

Australia ce kasa mafi karancin goggaggun 'yan kwallo a cikin wannan gasar.

Kasar wacce ta samu gurbinta daga yankin nahiyar Asiya ta zama ta biyu ne bayan Japan wacce ta ja ragama.

Haka kuma Mile Jedinak kyaftin din tawagar zai nemi ya farantawa kocinsa Ange Postecoglou rai domin a kasar ta haskaka a wannan gasar.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Mark Birighitti (Newcastle Jets), Eugene Galekovic (Adelaide United), Mitchell Langerak (Borussia Dortmund), Mat Ryan (Club Brugge).

'Yan wasan baya: Jason Davidson (Heracles Almelo), Ivan Franjic (Brisbane Roar), Curtis Good (Dundee United, on loan from Newcastle), Ryan McGowan (Shandong Luneng Taishan), Matthew Spiranovic (Western Sydney Wanderers), Alex Wilkinson (Jeonbuk Hyundai), Luke Wilkshire (Dinamo Moscow), Bailey Wright (Preston North End).

'Yan wasan tsakiya: Oliver Bozanic (Luzern), Mark Bresciano (Al Gharafa), Joshua Brillante (Newcastle Jets), James Holland (Austria Vienna), Mile Jedinak (Crystal Palace), Massimo Luongo (Swindon Town), Matthew McKay (Brisbane Roar), Mark Milligan (Melbourne Victory), Tommy Oar (Utrecht), Tommy Rogic (Melbourne Victory), Adam Sarota (Utrecht), James Troisi (Melbourne Victory), Dario Vidosic (Sion).

'Yan wasan gaba: Tim Cahill (New York Red Bulls), Ben Halloran (Fortuna Dusseldorf), Josh Kennedy (Nagoya Grampus 8), Matthew Leckie (FSV Frankfurt 1899), Adam Taggart (Newcastle Jets).