Rukunin C

Colombia:

Hakkin mallakar hoto AFP

Kocin Colombia Jose Pekerman na fuskantar babban cikas sakamakon raunin Radamel Falcao wanda rauni zai hana shi buga gasar.

Kasar ta samu gurbin zuwa gasar ce sakamakon kasancewa matakin na biyu a teburin yankin kudancin Amurka.

Sau hudu da kasar ta tsallake zuwa gasar cin kofin duniya, sau daya Colombia ta kai zagaye na biyu watau a shekarar 1990.

Tawaga:

Masu tsaron gida: David Ospina (Nice), Faryd Mondragon (Deportivo Cali), Camilo Vargas (Independiente Santa Fe).

'Yan wasan baya: Mario Yepes (AC Milan), Cristian Zapata (AC Milan), Pablo Armero (West Ham, on loan from Napoli), Camilo Zuniga (Napoli), Santiago Arias (PSV Eindhoven), Eder Alvarez Balanta (River Plate), Carlos Valdes (San Lorenzo).

'Yan wasan tsakiya: Fredy Guarin (Inter Milan), Juan Cuadrado (Fiorentina), James Rodriguez (Monaco), Abel Aguilar (Toulouse), Juan Fernando Quintero (Porto), Carlos Sanchez (Elche), Aldo Leao Ramirez (Morelia), Alexander Mejia (Atletico Nacional),

'Yan wasan gaba: Victor Ibarbo (Cagliari), Jackson Martinez (Porto), Carlos Bacca (Sevilla), Adrian Ramos (Hertha Berlin), Teofilo Gutierrez (River Plate).

Ivory Coast:

Hakkin mallakar hoto Associated Press

Ivory Coast na daga cikin kasashe biyu na Afrika da suka tsallake zuwa wannan gasar ba tare da an samu nasara a kansu ba.

Tawagar Elephant na da zaratan 'yan wasa kamar su Didier Drogba da Yaya Toure wadanda ta ke saran za su taimaka mata taka rawar gani fiye da abinda ya faru a gasar da aka buga a shekara ta 2010.

Kocin kasar Sabri Lamouchi wanda tsohon dan kwallon Faransa ne zai yi kokarin kafa tarihi ga wannan tawagar don kaiwa matakin akalla zagayen gabda na kusada karshe.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Boubacar Barry (Lokeren), Sylvain Gbohouo (Sewe Sport), Sayouba Sande (Stabaek).

'Yan wasan baya: Kolo Toure (Liverpool), Sol Bamba (Trabzonspor), Didier Zokora (Trabzonspor), Serge Aurier (Toulouse), Arthur Boka (Stuttgart), Ousmane Viera Diarrassouba (Caykur Rizespor), Constant Djakpa (Frankfurt), Jean-Daniel Akpa-Akpro (Toulouse).

'Yan wasan tsakiya: Yaya Toure (Manchester City), Cheick Tiote (Newcastle), Serey Die (Basel), Max Gradel (Saint Etienne), Diomande Ismael (Saint Etienne), Didier Ya Konan (Hannover), Mathis Bolly (Dusseldorf).

'Yan wasan gaba: Gervinho (Roma), Didier Drogba (Galatasaray), Salomon Kalou (Lille), Wilfried Bony (Swansea), Giovanni Sio (Basel).

Girka:

Hakkin mallakar hoto AP

Kwallaye hudu kacal a zura a ragar Girka a wasannin share fage na shiga wannan gasar amma duka da haka ta kasance ta biyu ne a rukuninta, inda Bosnia Herzgovina ta zama ta daya.

Tawagar Girka karkashin jagorancin Fernando Santos, ana kallonta a matsayin tawagar da ta fi kowacce rauni a nahiyar Turai.

Kasar wacce za ta sawa Konstantinos Mitroglou ido don haskakawa, na fatan yin maimaita abinda ta yi a gasar Turai ta 2004.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Orestis Karnezis (Granada), Panagiotis Glykos (PAOK), Stefanos Kapino (Panathinaikos).

'Yan wasan baya: Kostas Manolas, Giannis Maniatis, Jose Holebas (all Olympiakos), Sokratis Papastathopoulos (Borussia Dortmund), Giorgios Tzavellas (PAOK), Loukas Vyntra (Levante), Vasilis Torosidis (Roma), Vangelis Moras (Verona).

'Yan wasan tsakiya: Alexandros Tziolis (Kayserispor), Andreas Samaris (Olympiakos), Kostas Katsouranis (PAOK), Giorgos Karagounis (Fulham), Panagiotis Tachtsidis (Torino), Ioannis Fetfatzidis (Genoa), Lazaros Christodoulopoulos (Bologna), Panagiotis Kone (Bologna).

'Yan wasan gaba: Dimitris Salpingidis (PAOK), Giorgios Samaras (Celtic), Konstantinos Mitroglou (Fulham), Theofanis Gekas (Konyaspor).

Japan:

Hakkin mallakar hoto AFP

Kasar Japan ta samu damar buga wannan gasar ce bayan ta zama ta farko a rukunin kasashen nahiyar Asiya.

Japan wacce kocin tawagarta dan kasar Italiya ne zai nemi daga marbatar kasar a wannan gasar ganin cewar ana mata kallon daya daga cikin kasashen da za su wakilci nahiyar Asiya.

'Yan wasa kamar su Keisuke Honda, Shinji Kagawa da kuma Shinji Okazaki sune ake kallon za su taimakawa kasar ta taka rawar ganin a wannan gasar.

Masu tsaron gida: Eiji Kawashima (Standard Liege), Shusaku Nishikawa (Urawa Reds), Shuichi Gonda (FC Tokyo).

'Yan wasan baya: Masato Morishige (FC Tokyo), Yasuyuki Konno (Gamba Osaka), Yuto Nagatomo (Inter Milan), Maya Yoshida (Southampton), Masahiko Inoha (Jubilo Iwata), Atsuto Uchida (Schalke 04), Hiroki Sakai (Hannover 96), Gotoku Sakai (VfB Stuttgart).

'Yan wasan tsakiya: Yasuhito Endo (Gamba Osaka), Keisuke Honda (AC Milan), Shinji Kagawa (Manchester United), Makoto Hasebe (FC Nuremberg), Hiroshi Kiyotake (FC Nuremberg), Hotaru Yamaguchi (Cerezo Osaka), Toshihiro Aoyama (Sanfrecce Hiroshima), Manabu Saito (Yokohama F Marinos).

'Yan wasan gaba: Shinji Okazaki (Mainz), Yoichiro Kakitani (Cerezo Osaka), Yuya Osako (TSV Munich 1860), Yoshito Okubo (Kawasaki Frontale).