Holland na takaicin rashin Bale da Ramsey

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gareth Bale da Aaron Ramsey ba za su yi wasan sada zumunta tsakanin Wales da Holland ba.

Kocin Holland Lious van Gaal ya ce ya na jin takaicin rashin Gareth Bale da Aaron Ramsey a wasan da za su yi da Wales ranar laraba.

Bale, shahararren dan wasan kulob din Real Madrid mai shekaru 24, na fama da ciwon kafa tsawon makonni yayin da Ramsey mai shekaru 23 ya ke hutu.

Wasan sada zumuncin da za su buga a Amsterdam na daga cikin atisayen da kasar ta Netherlands ke yi don tunkarar gasar cin kofin kwallon duniya da za a yi a Brazil.

Van Gaal ya ce "na ja hankalin shugabannin kulob din da kada su yi wasa ba tare da Bale da Aaron Ramsey ba."

Ya kuma kara da cewa, "ya kamata a samu kwararrun 'yan wasa tun da muna da bukatar jajircewa, domin da zarar ba wadannan 'yan wasa biyu to, Wales ba ta da karfi."

Shi ma kocin Wales ,Chris Coleman na takaicin yin wasan ba tare da fitattun 'yan wasan biyu ba, inda a baya ya buga wasu wasannin ba tare da manyan 'yan wasa irin su Ashley Williams da Ben Davies ba.