Sebastian Larsson: An tsawaita kwantaraginsa.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sabestian Larsson ya rattaba hannu kan kwantaragin ci gaba da zama a Sunderland.

Dan wasan tsakiyar Sunderland Sebastian Larsson ya rattataba hannu kan tsawaita kwantaraginsa da za ta kare a 2017.

Dan wasan mai shekaru 28, wanda ya koma Wearside daga Birmingham a 2011, ya buga wa Sunderland wasanni 41 a wannan kakar.

Larsson dan kasar Sweden, ya ce, "ina son kasancewa a kungiyar, saboda naga alamu tana tafiya a kan hanyar da ta dace."

A watan Mayu, dan wasan ya taimaka wa kulob dinya tsira a gasar Premier inda suka yi nasarar cin wasanni biyar na karshe.

Cikin wannan fafutukar, Larsson ya ci kwallon da ta ba su nasara a wasansu da Man United a Old Trafford inda suka tashi 1-0.