Rukunin F

Argentina:

Hakkin mallakar hoto AP

Tawagar 'yan kwallon Argentina ta lashe gasar cin kofin duniya sau biyu (1978 da 1986) kuma a bana tanason ta kara bada mamaki ganin cewar tana da Lionel Messi da Gonzalo Higuain da kuma Angel Di Maria.

Kasar Argentina ba ta fuskanci wani tsaiko ba a kokarin samun gurbin hallatar wannan gasar musamman gannin cewar kocin tawagar Alejandro Sabella ya amfani da salon wasa 4-3-3.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Sergio Romero (Sampdoria), Mariano Andujar (Catania), Agustin Orion (Boca Juniors).

'Yan wasan baya: Pablo Zabaleta (Manchester City), Federico Fernandez (Napoli), Ezequiel Garay (Benfica), Marcos Rojo (Sporting Lisbon), Hugo Campagnaro (Inter Milan), Martin Demichelis (Manchester City), Jose Basanta (Monterrey).

'Yan wasan tsakiya: Javier Mascherano (Barcelona), Fernando Gago (Boca Juniors), Lucas Biglia (Lazio), Ricardo Alvarez (Inter Milan), Augusto Fernandez (Celta Vigo), Angel Di Maria (Real Madrid), Maxi Rodriguez (Newell's Old Boys), Enzo Perez (Benfica).

'Yan wasan gaba: Lionel Messi (Barcelona), Gonzalo Higuain (Napoli), Sergio Aguero (Manchester City), Rodrigo Palacio (Inter Milan), Ezequiel Lavezzi (Paris St-Germain).

Bosnia-Hercegovina:

Hakkin mallakar hoto Getty

Wannan ne karon farko da kasar Bosnia-Hercegovina za ta buga gasar cin kofin duniya, ta tsallake zuwa gasar bana bayan da ta zama ta daya rukuninta duk da cewar kasar Girka ma na cikin rukunin.

Dan wasan Manchester City Eden Dzeko shi ne babban dan wasan ta duk da cewar wannan rukunin da take mai sarkakiya ne saboda kasancewar Nigeria da Argentina a ciki.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Asmir Begovic (Stoke City), Asmir Avdukic (Borac Banja Luka), Jasmin Fejzic (VFR Aalen).

'Yan wasan baya: Emir Spahic (Bayer Leverkusen), Toni Sunjic (Zorya Lugansk), Sead Kolasinac (Schalke), Ognjen Vranjes (Elazigspor), Ermin Bicakcic (Eintracht Braunschweig), Muhamed Besic (Ferencvaros), Mensur Mujdza (Freiburg).

'Yan wasan tsakiya: Miralem Pjanic (Roma), Izet Hajrovic (Galatasaray), Haris Medunjanin (Gaziantepspor), Senad Lulic (Lazio), Anel Hadzic (Sturm), Tino Susic (Hajduk), Sejad Salihovic (Hoffenheim), Zvjezdan Misimovic (Guizhour Renhe), Senijad Ibricic (Erciyesspor), Avdija Vrsaljevic (Hajduk).

'Yan wasan gaba: Vedad Ibisevic (VfB Stuttgart), Edin Dzeko (Manchester City), Edin Visca (Istanbul BB).

Iran:

Hakkin mallakar hoto AP

Iran ba ta iya wuce zagayen farko ba a gasar cin kofin duniya uku da suka wuce (1978, 1998, 2006), kuma nasarar kasar a karon farko shi ne a wasanta da Amurka a shekarar 1998.

Tawagar Iran ta kunshi galibin 'yan wasa ne da ke murza leda a cikin kasar a yayinda take da kwararren koci watau Carlos Queiroz wanda ya taba jan ragamar Real Madrid da kuma kasar Portugal.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Daniel Davari (Eintracht Braunschweig), Alireza Haghighi (Sporting Covilha, on loan from Rubin Kazan), Rahman Ahmadi (Sepahan).

'Yan wasan baya: Hossein Mahini (Persepolis), Steven Beitashour (Vancouver Whitecaps), Pejman Montazeri (Umm Salal), Jalal Hosseini (Persepolis), Amir-Hossein Sadeghi (Esteghlal), Ahmad Alenemeh (Naft), Hashem Beikzadeh (Esteghlal), Mehrdad Pouladi (Persepolis).

'Yan wasan tsakiya: Javad Nekounam (Kuwait SC), Andranik Teymourian (Esteghlal), Reza Haghighi (Persepolis), Ghasem Haddadifar (Zob Ahan), Bakhtiar Rahmani (Foolad), Ehsan Hajsafi (Sepahan).

'Yan wasan gaba: Ashkan Dejagah (Fulham), Masoud Shojaei (Las Palmas), Alireza Jahanbakhsh (NEC Nijmegen), Reza Ghoochannejhad (Charlton), Karim Ansarifard (Tractor Saz, on loan from Persepolis), Khosro Heydari (Esteghlal).

Nigeria:

Hakkin mallakar hoto Getty

Wannan ne karo na hudu da Nigeria za ta buga gasar cin kofin duniya, duk da cewar ba ta taba wuce zagaye na biyu ba.

Bayan 'yan matsaloli a shekara ta 2012, Super Eagles karkashin jagorancin Stephen Keshi ta samu sauyi abinda ya bata damar lashe gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika a shekara ta 2014.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Vincent Enyeama (Lille), Austin Ejide (Hapoel Be'er Sheva), Chigozie Agbim (Gombe United).

'Yan wasan baya: Elderson Echiejile (Monaco), Efe Ambrose (Celtic), Godfrey Oboabona (Rizespor), Azubuike Egwuekwe (Warri Wolves), Kenneth Omeruo (Middlesbrough), Juwon Oshaniwa (Ashdod), Joseph Yobo (Norwich, on loan from Fenerbahce), Kunle Odunlami (Sunshine Stars).

'Yan wasan tsakiya: John Mikel Obi (Chelsea), Ramon Azeez (Almeria), Ogenyi Onazi (Lazio), Reuben Gabriel (Waasland-Beveren), Michael Babatunde (Volyn Lutsk).

'Yan wasan gaba: Ahmed Musa (CSKA Moscow), Shola Ameobi (Newcastle), Emmanuel Emenike (Fenerbahce), Michael Uchebo (Cercle Brugge), Peter Odemwingie (Stoke), Victor Moses (Liverpool, on loan from Chelsea), Uche Nwofor (Heerenveen).