Ingila na horo kan bugun fanareti

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan Ingila na gwaji kan yadda za su rinka cin bugun fanareti.

Kyaftin din Ingila Steven Gerrard ya bayyyana cewa 'yan wasan kasar sun fara gwajin bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida amma kuma ba za su yi sake da sauran fannonin wasan ba.

A manyan gasar wasanni goma da Ingila ta buga, shida daga cikinsu an karkare da bugun fanareti

Kyaftin Gerrard dai ya kasa cin fanareti a wasan dab da na kusa da karshe da suka yi da Portugal a shekarar 2006, amma ya ci da bugun tazara a wasan da suka yi da Italiya a gasar Euro 2012.

Gerrard ya ce "an shirya hakan ne saboda dan rashin nasarar da muka yi a baya amma wannan ba wani abin damuwa ba ne."

Ingila dai ta yi nasara a bugun daga kai sai mai tsaron gida a babbar gasar Euro 96, inda ta lashe kasar Spain.

Wani likitan kwakwalwa Dr Steve Peters zai taimaka wa tawagar 'yan wasan ta Ingila wajen saita tunaninsu domin samun natsuwa.