Ronaldo na fama da ciwon kafa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Christiano Ronaldo na fama da ciwon kwatangwalo

Hukumar kwallon kafa ta Portugal ta fadi ranar Laraba cewa dan wasan gaban kulob din Real Madrid, Christiano Ronaldo, na fama da ciwon gwiwa.

Hukumar ta FPF ta ce dan wasan, mai shekaru 29, ko da yake bai buga wasan da Portugal ta yi da Girka ba inda suka tashi canjaras ba ci a makon jiya, amma zai fara wasan motsa jiki na musamman ranar Litinin.

Gwarzon dan wasan na duniya ya samu kananan raunuka a kakar gasar da ta kare, amma duk da haka ya ci kwallo a wasan karshe na Zakarun Turai da Real Madrid ta samu nasara.

A gasar cin kofin duniya da za a gudanar a Brazil, kasar Portugal za ta fara fafatawa ne da kasar Jamus a Salvador ranar 16 ga watan Yuni.