Jaaskelainen: Sabon kwantaragi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jaaskelainen zai ci gaba da zama a West Ham zuwa shekarar 2015

Mai tsaron gidan West Ham Jussi Jaaskelainen ya sanya hannu kan sabon kwantiragin shekara daya da zai ba shi damar ci gaba da zama a kungiyar zuwa 2015.

Jaaskelainen mai shekaru 39, ya shiga kulob din West Ham a tsarin musayar 'yan wasan nan da ba biyan kudi, bayan ya kwashe shekaru 14 a Bolton inda ya yi wasanni 18 a gasar Premier a shekarar 2013-14.

Amma a karshen kakar, Andrian ya zama mai tsaron gida na farko da West Ham ta fara muradi bayan ajiye Jaaskelainen a watan Janairu.

Jussi ya bayyana a shafin sadarwa intanet na West Ham cewa, "ina jin dadin jikina kuma na ji dadi a kakar gasar da a ka kammala, ina kuma fatan dorawa daga inda na tsaya."