Fabregas: Arsenal ta ce a kai kasuwa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Arsenal ta ce wa Barcelona ba ta bukatar Cesc Fabregas

Arsenal ta ce ba za ta aiwatar da yarjejeniyar da ta yi da Barcelona ba ta sake sayen tsohon dan wasanta Cesc Fabregas ba, wanda hakan ya bude kofa ga sauran kungiyoyi.

Arsenal ta gindaya sharadin sake sayar mata da dan wasan a lokacin da ta sayar wa Barcelona shi a 2011 kan fam miliyan 35 amma Barcelona ta yi watsi da bukatar Arsenal din tun farko da ta ce zai iya tafiya.

Sauya shawarar da zakarun kofin FA din suka yi yanzu ta yi watsi da maganar dawo da dan wasan ya bude kofa ga abokan hamayyar Arsenal din su sayi dan wasan da ke tawagar Spaniya ta gasar Kofin Duniya.

Burin Arsenal dai yanzu shi ne samun dan wasan gaba da zai yi gogayya da Olivier Giroud da dan baya da zai maye gurbin Bacary sagna da kuma mai tsaron gidan da shi ma zai maye wurin Lukasz Fabianski.