Fifa: Algeria ta zama ta daya a Afrika

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption A duniya Jamus na matsayin ta biyu sai Brazil sai sai Uruguay sai Colombia sai Italia sai kuma Ingila ta goma.

Algeria ta zama ta daya a Afrika a jadawalin Fifa na kasashen duniya da suke gaba a kwallon kafa, yayin da Spain ta ci gaba da zama ta daya a duniya.

Sakamakon ya fito ne bayan Algerian wadda kuma ta zama ta 22 a duniya ta yi nasara a wasanni uku a jere na shirin tunkarar gasar duniya.

Ivory Coast wadda kafin wannan jadawalin ta dade a matsayin ta daya a Afrika ta koma ta biyu kuma ta 23 a duniya.

Masar ta samu gagarumin koma-baya inda ta fado daga ta 24 zuwa ta 36 a duniya, amma ta uku a Afrika.

Ghana ta 4 a Afrika ta 37 a duniya; Cape Verde ta 39 ta 5 a Afrika, yayin da Najeriya ta 44 a duniya ta 6 a Afrika.

Tunisia ta 48 ta zama ta 7 a Afrika; Guinea ta 52 ta 8 a Afrika; Sierra Leone a duniya ta 54 a Afrika ta 9, Kamaru ta 56 a duniya ta 10 a Afrika.

Karin bayani