Rooney: zan yi wasa a ko wane bangare

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Rooney ya ce yana alfahari ya buga wa Ingila wasa kuma hakan ba zai sauya ba ko da ba a sa shi a wasa ba

Wayne Rooney ya ce ba zai damu ba a duk bangaren da aka sa shi ya yi wa Ingila wasa a gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil.

Dan wasan gaban na Man United mai shekara 28, ya samu nasarar cin kwallo duk da sa shi a wani sabon bangare a wasan da Ingila ta yi da Ecuodor ranar Laraba da suka tashi 2-2.

Rooney ya ce, "ina jin dadin buga wa kasata wasa ko da kuwa ta bangaren hagu ko dama ne, tsakiya ko can gaba."

Rooney ya ci wa Ingila kwallaye 40 a wasanni 91 da ya buga wa kasar, amma kuma bai taba ci mata kwallo ba a wasanni takwas na gasar kofin duniya da ya buga a 2006 da 2010.

Dan wasan ya ce bayan shi, Ingila na da wasu zaratan 'yan wasan gaba da su ka hada da Sturridge da Lambert da Welbeck da kuma Raheem Sterling saboda haka dole ya jajirce.