Qatar za ta dauki mataki kan gasar 2022

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an Qatar sun ce an zuba jarin da ya kai fam miliyan 23 a shirye-shiyen gudanar da gasar.

An yi amanna cewa jami'an Qatar za su dauki kowane mataki ciki har da na shari'a, matukar aka sake kada kuri'ar karbar bakuncin gasar kofin duniya a 2022.

Ana zargin an aikata rashawa a wajen tantance wanda ya cancanci karbar bakuncin, abin da ya kai ga kiraye-kirayen a sake kada kuri'a ko a gano inda matsalar take.

Qatar ta musanta zargin aikata ba daidai ba, amma yanda lamarin zai kaya ya ta'allaka ne kan binciken da jami'in hukumar FIFA Micheal Garcia zai yi.

Mr. Garcia, wanda Ba-Amirke ne kuma lauya, zai kammala bincikensa a ranar 9 ga watan Yunin da muke ciki.

Shi ma shugaban Uefa Michel Platini wanda ya goyi bayan Qatar ta karbi bakuncin gasar, ya bi sahun mataimakin Shugaban Fifa Jim Boyce inda ya amince a sake zaben matukar aka tabbatar da zargin bayar da toshiyar baki.