Kofin Duniya:Jennifer Lopez ta ja baya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Pitball da Leitte za su yi wakar ba tare da Jennifer Lopez ba

Jennifer Lopez ta fice daga cikin mawakan da za su rera wakar bude gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil.

Jami'an Fifa sun ce mawakiyar ba za ta halarci bikin bude gasar ba, saboda wasu dalilai da ba a bayyana ba da suka danganci aikin hada waka.

A da an tsara Lopez za ta yi waka tare da mawakin kidan gambaran nan na rap, Pitbull da mawakiyar nan ta Brazil Claudia Leitte wadda ta yi wakar 'We are One' (ole Ola) da ita.

Bikin bude gasar na tsawon mintoci 25 zai kunshi mawaka da masu wasanni iri daban-daban su 600.