"Rooney na firgita sauran kasashe"

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rooney ya ci kwallaye 39 a gasar wasanni 91 da halarta.

Fitaccen dan wasan Ingilan nan, David Beckham ya ce wayne Rooney wani sinadari ne da zai taimaka wa Ingila a gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil saboda ya riga ya gama tsoratar da abokan karawarsu.

Sai dai akwai shakku kan dan wasan mai shekaru 28, ganin ya yi wasanni 8 a gasar cin kofin duniya da ya halatta amma bai taba cin kwallo ba.

Beckham, tsohon dan wasan gaban Ingila ya bayyana cewa, "ko Rooney bai ci kwallo ba, to zai taimaka ko ya yi sanadin da za a ci, ko kuma ya yi wa kasarsa aiki tukuru."

David Beckham ya kuma yi imanin cewa dan wasan gaban, ya taimaka wa Man United a kakar da ta kare duk kuwa da gwagwamaryar da suka yi da takwaransa Paul Scholes wanda ya ba da shawarar a ajiye shi.