Joe Cole ya koma Aston Villa

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Cole ya ce ya samu nasarori da yawa a fagen rayuwarsa, amma har yanzu ya na da ragowa.

Kungiyar Aston Villa ta kulla kwantaragin shekaru biyu da dan wasan tsakiya na West Ham Joe Cole.

Dan wasan mai shekaru 32 wanda ya ci kwallaye 56 ba shi da wata kungiya bayan da kwantiraginsa da West Ham ta kare a watan Mayu.

Ya ce, ''wannan kulob din mai karfi ne, yana kuma da wata gagarumar dama da zai kara bunkasa.''

Cole, wanda ya yi wasa a Chelsea da Liver pool a ka kuma ba da shi aro ga Lille, ya zama dan wasa na biyu da Villa ta dauka a wannan bazarar.

Kocin Aston Villa din Paul Lambert ya kuma dauki tsohon dan wasan bayan Arsenal Philippe Senderos wanda shi ma kwantaraginsa ta kare da Valencia.