Qatar 2022: Fifa za ta tattauna yau

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Qatar ta musanta zargin ba da toshiyar baki a kokarin da ta yi na a ba ta damar daukar nauyin gudanar da gasar.

Fifa, za ta yi zama ranar talata a birnin Soa Paulo na Brazil inda za ta tattauna batun zargin ba da cin hanci wurin zaben da a ka yi wa Qatar na karbar bakuncin gasar kofin duniya a 2022.

Taron tattaunawar ya zo ne kwana daya da shugaban hukumar kwallon kafar ta duniya, Sepp Blatter ya zargi kafafen yada labarai na Birtaniya da nuna wariyar launin fata ta hanyar yada zarge-zargen.

Wakilin BBC ya ruwaito cewa, yayin da wasu ke ganin cewa Fifa ba za ta dawo da martabarta ba har sai Blatter ya sauka daga shugabancinta, Blattern har yanzu na da tagomashi a idon sauran jami'an hukumar.

Sai dai duk da haka, biyar daga cikin masu daukar nauyin gasar ta kofin duniya sun bukaci a gudanar da cikakken bincike kan batun zargin.

Karin bayani