Kofin Duniya: Hodgson ya gargadi Ingila

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A ranar Asabar ne Ingila za ta fara wasanta da Italiya a Manaus.

Kocin Ingila Roy Hodgson ya yi gargadin da a rage doki a kan tawagar 'yan wasan kasar da ta kunshi matasan 'yan wasa da za su je gasar kofin duniya a Brazil.

Hodgson mai shekara 66 ya ce,'' bari mu ga irin kokarin da za su yi idan sun je buga wa Ingila gasar, kafin mu yabe su.''

Kocin ya ce 'yan wasan nasa na cike da nishadi da burin tunkarar gasar ta duniya, amma duk da haka ya ce, dole ne a yi taka-tsan-tsan.

Duk da zaratan matasan 'yan wasan da tawagar ta kunsa da suka hada da Alex Oxlade-Chamberlain da Sterling Raheem da kuma Barkley, Hodgson na ganin har yanzu wasunsu na bukatar kara zage damtse.