Mourinho: Kiris na zama kocin Ingila

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mourinho ya bayyana cewa 'yan wasa irin su Frank Lampard da John Terry da Ashley Cole su suka dauki hankalin sa a kokarin zama kocin na Ingila.

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce saura kiris ya zama kocin Ingila a 2007, amma matarsa ta fada masa cewa zai yi hasarar wasannin sauran kulob-kulob din kwallon kafa na yau da kullum.

A lokacin, Ingila ta sallami kocinta Steve McClaren bayan ya gaza kai kungiyar gasar Euro 2008 yayin da kuma wa'adin kwantaragin Mourinho ta farko ta kare a Stamford Bridge a watan Satumba.

Mourinho ya ce, "saura kiris na zama kocin Ingila, amma ta hana ni. Hakika matata ta yi dai-dai."

Kocin dan Kasar Portugal, a karshe ya kama aiki da Inter Milan inda kuma Fabio Capello ya zama kocin Ingila.