'Neymar na fuskantar matsin lamba'

Hakkin mallakar hoto VIPCOMM
Image caption 'Yan Brazil sun sawa Neymar ido

Gawurtaccen dan kwallon Brazil, Pele ya bayyana cewar Neymar na fuskantar matsin lamba don ya kai kasar ga nasara a gasar cin kofin duniya.

Neymar mai shekaru 22, bai taba buga gasar cin kofin duniya ba, amma kuma zura kwallaye bakwai a wasanni tara da Brazil ta buga.

Pele ya ce "Neymar matashin dan kwallo ne, amma yana fuskantar matsin lamba kan sauke nauyin da ke kansa".

Brazil ta lashe gasar cin kofin duniya sau biyar amma kuma rabon da ta lashe gasar tun a shekara ta 2002.

Kasar wacce za ta dauki bakuncin gasar za ta fuskanci Croatia a birnin Sao Paulo a wasan farko a ranar Alhamis.

Neymar na cikin tawagar Barcelona wacce ke haskakawa a gasar kwallon Turai.

Karin bayani