Ronaldo na yi wa Klose mugun fata

Image caption Shi kuwa Klose ya ce kawar da tarihin Ronaldo na daya daga cikin burinsa a Brazil.

Tsohon gwarzon dan wasan Brazil da ya fi kowana dan wasa cin kwallo a tarihin kofin duniya Ronaldo yana fatan Klose na Jamus ya kasa kawar da bajintarsa a gasar da za a yi a Brazil.

Ronaldo mai shekaru 37 ya ci kwallaye 15 a gasar kofin duniya uku, inda ya wuce 'yan wasan Jamus Gerd Muller da shi Klose da kwallo daya.

Da yake jawabi a wurin bikin magoya bayan kungiyar kasar Brazil, a Fortaleza, Ronaldo ya bukaci magoya bayan da su yi wa Klose wani abu da zai hana shi cin kwallo.

Ronaldo, ya ce, ''zai yi duk addu'ar da zai iya domin ganin Klose bai kawar da wannan tarihi da ya kafa ba.

Duk da damar da dan wasan yake da ita cewa har yanzu shi yana wasa, amma duk da haka ba zai iya kawar da tarihin ba.''

Karin bayani