Ingila ce ta uku a 'yan wasa masu tsada

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption kiyasin da aka yi, darajar kasashen 32 da za su fafata a gasar ya kai fam biliyan 6.2.

Rahotanni sun bayyana cewa, Ingila ita ce ta uku wadda 'yan wasan da ke tawagarta ke da tsada inda ta ke bin bayan kasar Jamus da Sipaniya.

Kiyasin adadin kudin Inshorar 'yan wasan na fam miliyan 550 da aka yi, ya nuna cewa darajar tawagar Ingila ta ninka ta kasar Italiya sau uku.

Wani bincike da Lloyds da kuma cibiyar bincike kan tsimi da tanadi da harkokin kasuwanci suka gudanar, ya nuna cewa darajar dan wasan Ingila daya, ya fi dukkanin tawagar 'yan wasan Costa Rica.

An dai hada yawan kudaden Inshorar ne karkashin yawan kudin da kulob din ke samu da ma na 'yan wasan 23 da ke cikin tawagar ta Ingila.