Chelsea ta sayi Fabregas

Hakkin mallakar hoto CHELSEA FC
Image caption Fabregas ya ce, ''na zaku in fara buga wa Chelsea wasa''

Chelsea ta sayi tsohon dan wasan Arsenal Cesc Fabregas daga Barcelona na tsawon shekara biyar.

Dan Spania mai shekaru 27, ya yi shekaru uku a Barca kafin ya komo Chelsea bayan da Arsenal ta ce ba za ta sake sayensa ba.

Ko da ike ba a bayyana kudin sayen nashi ba, amma ana ganin ya kai fam miliyan 30.

Fabregas wanda yake cikin tawagar Spaniya ta gasar kofin duniya ya ce, Chelsea ta dace da burinsa na kwallon kafa.

Dan wasan ya ce ya duba tayin sauran kungiyoyi amma ya ga Chelsea ta fi dacewa, ya kara da cewa yana da sauran aikin da bai kammala ba a Premier.