Thailand: Kallon gasar 2014 kyauta ne

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojoji sun bukaci hukumar kula da kafafan yada labarai ta yi cinikin wasannin don nunawa kyauta.

Gwamnatin sojin Thailand ta umarci masu gidajen talabijin da su tabbatar cewa ma'abota kwallon kafa ba su biya kudi don kallon gasar cin kofin duniya ba.

Sojin sun ce hakan na daga matakan nuna farin ciki da suka hada da yi wa mutane aski da shiga wuraren kallon wasanni kyauta.

Wakilin BBC da ke Bangkok Jonathan Head ya ce, tabbatar da cewa mutane sun kalli gasar shi ne wani abu mafi muhimmaci a matakan nuna farin ciki.

Sai dai tuni kafar yada labarai ta RS ta sayi damar mallakar nuna wasannin, amma ta shirya ba da damar nuna kashi uku cikin adadin wasannin da za a yi a gasar kyauta.

Rahotanni sun bayyana cewa RS na bukatar a biya ta diyyar dala miliyan 21.5 in har ana son ta ba da damar nuna wasan kyauta.