Australia ta sha kashi a hannun Chile

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Farmakin da Chile ke kaiwa ya nuna cewa har yanzu fa ba kanwar lasa ba ce.

A wasan farko tsakanin Chile da Australia na cin kofin duniya, Alex Sanchez ya ci kwallo daya tare da taimaka wa aka ci ta biyu.

Sanchez ya yi nasarar cin kwallon ne mintuna 12 da fara wasa ya kuma gyara wa Jorge Valdivia wanda ya kara ci mintuna biyu da cin ta farko.

Bayan dawo wa daga hutun rabin lokaci Wigan's Jean Beausejour ya jefa kwallo ta uku a ragar Autralia.

Sakamakon rawar da 'yan wasan bayan Chile irin su Gary Medel da Gonzalo Jara suka taka, ya taimaka wajen mayar wa Autralia hannun agogo baya a gasar ta bana.