Fifa ta dakatar da Beckenbauer

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Ya kuma rike mukamin Kyaftin a tawagar 'yan wasan Jamus lokacin da ta karbi bakuncin gasar a 1974 inda suka ci kofin.

Fifa ta dakatar da tsohon dan kwallon kafar nan Franz Beckenbaue daga duk harkokin kwallon kafa saboda laifin kin bada hadin kai a binciken da ake na zargin cin hanci wajen bai wa Qatar karbar bakuncin gasar kofin duniya 2022.

Beckenbauer mai shekaru 68, wanda ya ci kofin duniya lokacin yana buga wasa a Jamus a 1974, ya kuma zama koci a 1990 inda aka bukace shi ya taimaka a gudanar da bincike karkashin jagorancin Michael Garcia wani Lauya dan kasar Amirka.

Shi dai Beckenbauer na daga cikin shugabannin kwamatin da ya zabi kasar Russia na karbar bakuncin gasar kofin duniya a 2018 da kuma Qatar a 2022 an dakatar da shi har kwanaki 90.

Fifa ta bayyana cewa Benckenbauer ya ki amsa kiran da aka yi masa na taimaka wa don gudanar da bincike kan yadda aka yi wajen bada damar karbar bakuncin gasar kofin duniyar a 2018 da kuma 2022.