Luiz ya koma Paris St-Germain

Hakkin mallakar hoto VIPCOMM
Image caption David Luiz ya haskaka a wasan Brazil da Croatia

Paris St-Germain ta sanarda kamalla cinikin dan kwallon Chelsea, David Luiz don taka leda na tsawon shekaru biyar a Faransa.

Dan Brazil din mai shekaru 27 zai hade da kungiyar bayan kamalla gasar cin kofin duniya.

Luiz ya ce "Tun a lokacin da Paris St Germain ta tuntube ni, hankali na ya karkata".

Dan wasan ya koma Chelsea ne daga Benfica a kan fan miliyan 21.3 a shekara ta 2011 kuma ya bugawa kungiyar wasanni 143.

Tuni Chelsea ta saye Cesc Fabregas daga Barcelona sannan tana gabda kamalla cinikin dan wasan Atletico Madrid Diego Costa.

Karin bayani