Brazil : Holland ta lallasa Spain

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Spain da Holland suna rukunin Group B ne a gasar ta 2014 da ake gudanarwa a Brazil

A ci gaba da wasan share fage na gasar cin kofin duniya da a ke a Brazil, kasar Holland ta lallasa Spain wadda ke rike da kofin da ci 5-1 a rukunin Group B inda Robin van Persie da Arjen Robben kowannen su ya ci kwallo 2.

Dan wasan Spain Xabi Alonso ne ya fara daga ragar Netherland kafin daga bisani Van Persie ya farke inda ya ci kwallon da ka kafin tafiya hutun rabin lokaci

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, Robben ya ci kwallo 2 sai Stefan De Vrij header Van Persie's wadanda suka ci ragowar kwallayen.