Mourinho: Lalle za mu sayi Costa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Costa haifaffen Brazil, ya ci wa Atletico Madrid kwallaye 36 a wasanni 52 a bana, suka dauki La Liga a karon farko tun 1996.

Mourinho ya bayar da tabbacin cewa har yanzu Chelsea na son sayen Diego Costa dan Spain na Atletici Madrid.

Chelsea ta so kammala sayen dan wasan mai shekara 25 a kan fam miliyan 32 kafin gasar kofin duniya.

Rashin cimma wa'adin bai sa Mourinho ya karaya ba kan sayen dan wasan da yake cikin tawagar Spain da Holland ta ci 5-1 ranar Juma'a.

Mourinho, ya ce, ''ina da cikakken kwarin guiwa za mu same shi a karshe zai dwo wurinmu.''

Ya ce, ''Costa dan wasa ne da nake so a kungiyata. Kuma na bukaci kungiyar ta kawo shi.''

Diego Costa haifaffen Brazil, ya ci wa Atletico Madrid kwallaye 36 a wasanni 52 a bana, suka dauki La Liga a karon farko tun 1996.