Mourinho: Courtois zai dawo Chelsea

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mourinho ya kawo karshen jita-jitar komawar Courtois Real Madrid

Mourinho ya tabbatar cewa mai tsaron gidan Belgium Thibaut Courtois zai dawo Chelsea bayan aro na shekara uku a Atletico Madrid.

Golan mai shekara 22 ya taimaka wa kungiyar ta Spaniya ta dauki La Liga bana kuma ta kai wasan karshe na zakarun Turai.

Mourinho wanda ya kai ziyarar taimako Ivory Coast, ya ce da zarar an gama gasar kofin duniya kai tsaye courtois zai taho Chelsea.

Golan ya kama wa Atletico Madrid a wasan kusa da karshe na zakarun Turai da suka fitar da ainahin kungiyarsa Chelsea.

Kafin kuma Real Madrid abokiyar hamayyarsu ta La Liga ta yi galaba a kansu a wasan karshe na zakarun Turan.

Yanzu dai golan yana shirin wasan farko na Belgium na Group H na kofin duniya da za ta yi da Algeria ranar Talata.

Karin bayani