Switzerland ta doke Ecuador

Hakkin mallakar hoto Epa
Image caption Switzerland ta yunkuro daga baya ta yi galaba a kan Ecuador

Switzerland ta ci Ecuador 2-1 a wasan farko na kasashen na gasar kofin duniya da ake yi a Brazil a rukunin Group E.

Ecuador ce ta fara jefa kwallo a raga a minti na 22 ta hannun Enner Valencia.

Admir Mehmedi, da ya shigo daga baya, shi ya rama wa Switzerland bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 48.

Bayan cikar mintina 90 na wasan, ana dab da tashi Seferovic wanda shi ma daga baya aka sa shi, ya kara cin Ecuador