Faransa ta doke Honduras 3-0

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Benzema ne ya ci kwallaye biyu ta ukun kuma da ya kai hari mai tsaron gidan ne ya ci kansu a kokarin kamo ta

Faransa ta doke Hondurs da ci 3-0 a wasansu na farko na gasar cin kofin duniya na rukunin Group E.

Benzema ne ya fara ci da bugun fanareti ana dab da tafiya hutun rabin lokaci.

Bayan an dawo daga hutun ne kuma sai mai tsaron gidan Honduras Valladares ya ci kansu kwallo ta biyu a minti na 48 bayan da kwllon da Benzem ya buga ta doki turken raga ta dawo ta subuce daga hannunsa da ya kasa kamata ta fada raga.

A kwallon ta biyu ne aka fara amfani da fasahar nan da aka bullo da ita a gasar ta tantance shigar kwallo raga.

Can kuma a minti na 72 ne dan wasan na Real Madrid ya kara jefa kwallo ta uku a ragar Honduras din.

Da wannan nasara Faransa ce ta daya a rukunin da maki uku da kwallaye uku sai Switzerland ita ma da maki uku amma bambamcin kwallo daya.

Ecuador tana matsayi na uku ba maki da bashin kwallo daya Honduras na ta hudu da bashin kwllaye uku.