Ingila ta rasa Gary Lewin

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kakakin FA ya ce ba su da matsala dangane da rashinsa saboda akwai Steve Kemp.

Mai ba wa 'yan wasan Ingila horon motsa jiki Gary Lewin ba zai sake aiki ba a lokacin gasar cin kofin duniya da ake yi a Brazil ba sakamakon targaden da ya yi.

Lewin ya yi targaden ne lokacin da yake murnar kwallon da Daniel Sturridge ya rama wa Ingila bayan da Marchisio ya ci su.

Kocin Ingila Roy Hodgson ya ce, jami'in ya taka robar ruwa ne da ya yi tsalle daga nan ne ya gurde a idon kafa.

Kakakin hukumar kwallon kafa ta Ingila FA ya ce ba su da matsala dangane da rashinsa saboda akwai wani mai ba da horon Steve Kemp.

Italiya ta yi nasara a wasan bayan da tsohon dan wasan Man City Mario Balotelli ya kara ci wa Italiya ta kwallo biyu.