'Yan wasan Najeria za su sha kudi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a ba wa kowane dan wasan Najeria sama da Naira miliyan hudu idan suka dauki kofin duniya

Za a ba kowanne daga cikin 'yan wasan Najeriya 27 da ke gasar cin kofin duniya dala 102 500, sama da Naira miliyan 17 domin cin kofin na duniya.

Hukumar kwallon kafa ta kasar ce ta sanar da haka, da cewa a yanzu an sasanta duk wata sa-in-sa kan maganar kudin da za a rika ba su.

Duk wasan da suka yi nasara a karawar rukuni za a ba kowa dala 10,000 kwatankwacin Naira miliyan 1 da dubu 6000 a zagaye na biyu kuma za a ba kowa dala 12,500.

Idan kuma suka yi nasara a wasan dab da na kusa da karshe kowana dan wasa zai karbi dala 15,000, a wasan kusa da karshe kuwa za su samu dl 20,000.

Idan kuwa har suka kai ga daukar kofin na duniya kowane dan wasa zai tsira da dala 25,000.

Rabon Najeriya ta kai zagaye na biyu na gasar kofin duniya tun 1998, kuma tun wannan lokacin rabonta da cin ko da wasa daya a gasa biyu da ta halatta.

A ranar Litinin Najeriya za ta kara da Iran a rukuninsu na Group F.

Hukumar kwallon kafa ta duniya ta ba wa kowace kasa da kai zuwa gasar ta kofin duniya dla miliyan 1.5 domin shiryawa, kuma kowace kasa da ta je za ta samu akalla dala milina takwas.

Karin bayani