USA da Ghana sun tashi 2-1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ghana ta samu damammaki da yawa na cin kwallaye amma ba ta iya ci ba saboda rashin sa'a.

USA da kasar Ghana da ke rukuni Group G sun buga wasan su na farko inda aka tashi wasan da ci 2-1.

Kasar Amirka ce ta fara zura kwallon farko minti biyu da sa wasa ta hannun Dempsey. Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci an yi ta dauki- ba-dadi ta hanyar kai hare-hare musamman Ghana.

Saura mintuna 8 takwas lokaci ya cika, mai lamba 10 dan kasar Ghana A Awey ya samu nasarar farke kwallon.

Amirka ta ci kwallo ta biyu a mintuna na 88 ta hannun Brooks bayan da aka yi bugun gefe shi kuma ya ci kwallon da ka.