Nigeria da Iran sun tashi babu ci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan Nigeria sun fi rike kwallo

Nigeria ta tashi babu ci a wasanta na farko a gasar cin kofin duniya tsakaninta da Iran a karawar da ta yi a birnin Curitiba na Brazil.

'Yan wasan Super Eagles sun fi rike kwallo a wasan amma kuma suka kasa zura kwallo.

Ogenyi Onazi da Ahmed Musa da kuma Shola Ameobi duk sun kuskure da sun shigar da Nigeria gaba a wasan.

A bangaren Iran kuwa Reza Ghoochannejad shi ne ya kai hari mafi hadari amma kuma golan Super Eagles Vincent Enyeama ya kabe ta.

Ke nan a yanzu Argentina ce kan gaba a rukunin, sai Nigeria da Iran a matsayin na biyu a yayin da Bosnia ke matakin karshe.

Karin bayani