Najeriya ta yi canjaras da Iran

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rabon Najeriya da Iran su ci kwallo a gasar cin kofin duniya tun 1998.

A dai ci gaba da wasan gasar cin kofin duniya da ake a Brazil, Najeriya ta yi nata wasan da kasar Iran sun tashi canjaras ba bu ci.

An kammala zangon farko na wasan ba inda aka ci.

Kasashen sun yi ta kai wa juna hari bayan an dawo daga hutun rabin lokaci amma duk da haka sun tashi a wasan 0-0.

Tun da farko, kafin buga wasan, 'yan Najeriya sun ci borin yin wasan kura da kasar ta Iran amma wanki hula ya kai su dare.