Kofin duniya: Nigeria za ta kara da Iran

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria na cikin rukunin F a gasar cin kofin duniyar

Yayin da ake ci gaba da gasar cin kofin duniya a kasar Brazil, tawagar kwallon kafa ta Super Eagles ta Nigeria za ta kara da takwararta ta Iran.

Taka ledar ta ranar Litinin za a yi ta ne da misalin karfe 8 na dare agogon Nigeria, a dandalin wasa na Curitiba.

Ita ma kasar Ghana da ke runkunin G za ta kece raini da Amurka, a gasar cin kofin duniyar.

Tawagar Super Eagles su ne 'yan wasa mafiya karancin shekaru a gasar ta Brazil, inda 'yan wasa 15 a cikinsu ba su wuce shekaru 25 ba.