Ronaldo: Zan iya wasanmu da Jamus

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An yi ta rade radin cewa dan wasan ba zai iya wasannin gasar kofin duniya ba saboda raunukan da yi fama da su

Cristiano Ronaldo ya ce ya murmure daga ciwon guiwar da ya yi fama da shi a makwannin nan kuma zai iya wasansu da Jamus.

Dan wasan wanda aka gan shi a lokacin atisaye da wani daurin bandeji a guiwarsa ta hagu, ya ce shi ne na farko da zai gaya wa kocinsu Paulo Bento idan ba zai iya wasan ba.

Dan wasan na gaba na Real Madrid shi ne zai yi kyaftin din tawagar 'yan wasan Portugal a karawar da za su yi da Jamus, a wasansu na farko na rukunin Group G a Salvador ranar Litinin din nan.