An sallami Schumacher daga asibiti

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Likitoci sun ba shi maganin fita hayyaci har sau bakwai don rage masa kumburi a kwakwalwa.

Iyalan zakaran gasar tseren Motoci ta Formular 1, Michael Schumacher sun ce dan wasan ya bar asibitin Grenoble da ke Faransa kuma yanzu haka yana cikin hayyacinsa.

Jami'ai sun ce an mayar da dan wasan mai shekaru 45 zuwa asibitin jami'ar Lausanne da ke kasar Switzerland.

An bai wa Schumacher maganin fita hayyaci ne bayan ya samu wani mummunan rauni a kansa, lokacin da ya yi da hatsari yana wasan sulun kankara a tsaunin Alps na Faransa a karshen shekarar da ta gabata.

Likitoci sun bai wa zakaran tseren na duniya karo bakwai, maganin fita hayyacin don rage masa kumburi a kwakwalwa.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a madadin iyalansa, Manajar Schumacher, Sebine Kehm ta ce Michael ya bar asibitin Grenoble don ci gaba da wartsakewa a wani kebabben wuri.