"Batun Rooney ka iya yi mana illa"

Frank Lampard Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cece-kuce kan Rooney ya mamaye kafafen yada labarai a Ingila

Cece-kuce da "adawa" da Wayne Rooney ka iya yin illa ga tawagar Ingila a gasar cin kofin duniya, a cewar Frank Lampard.

Anta yin maganganu kan makomar Rooney a tawagar bayan da aka sanya dan wasan ya taka leda ba a gurbin da ya saba ba, a wasan da Italy ta doke su.

"Cece-kuce akan dan wasa guda - daya daga cikin 'yan wasanmu da suka fi muhimmanci - ba abu ne mai kyau ba," a cewar Lampard mai shekaru 35.

Frank Lampard na bukatar ganin an daina "adawa ko makarkashiyar" da ake nuna wa Wayne Rooney.

Dan wasan gefe Raheem Sterling, wanda ya maye gurbin da Rooney ke bugawa, ya ce mayar da su ga guraben da suka saba taka leda a wasansu da Uruguay ranar Alhamis zai yi kyau.

Karin bayani