"'Yan wasanmu ba su yi bore ba"

Image caption Ghana za ta kara wasanta na gaba da Jamus

Hukumar kula da kwallon kafa ta Ghana ta musanta rahotannin da wani gidan radio a kasar ya bayar na cewa an samu sabani a tsakanin tawagar Black Stars bayan da Amurka ta doke su da ci 2-1 a gasar cin kofin duniya.

A cewar Joy FM, "boren 'yan wasa ne" ya tilastawa Ghana ta soke taron manema labaran da ta shirya a ranar Talata.

Hukumar ta GFA ta ce: "Mun bayyana a zahiri cewa wannan labarin karya ne kuma ba shi da tushe".

"Babu wani bore da 'yan wasa suka yi wa kocin Black Stars Kwesi Appiah."

Sanarwar ta kara da cewa: "Babu wani dan wasa ko 'yan wasa da suka yi bore.

Karin bayani