Netherlands ta doke Australia 3-2

Netherlands ta doke Australia 3-2 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Netherlands ta sha wuya kafin ta kai ga doke Australia 3-2

Kasar Netherlands na daf da kaiwa zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya bayan da kwallon da Memphis Depay ya zura ta basu damar doke Australia da ci 3-2.

Arjen Robben ne ya fara zira kwallo a ragar Australia, sai dai ba da jimawa ba Tim Cahill ya rama mu su.

Mile Jedinak ya saka Australia a gaba ta hanyar bugun fanareti kafin Robin van Persie ya farke musu - inda ya mayar da wasan 2-2.

Daga nan ne kuma Mathew Leckie ya barar da damar zira kwallo ta uku ga Australia, sai kuma Depay ya narka wata kwallo daga yadi na 25 abinda ya baiwa Holland nasara.

Karin bayani