Man City za ta kara da Newcastle

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kocin City, Manuel Pellegrini ya haskaka a bana

Zakarun gasar Premier ta Ingila Manchester City za ta soma kare kambunta na gasar a kakar wasan 2014/2015 da karawa tsakaninta da Newcastle.

Za a soma gasar a ranar 16 ga watan Agusta, a yayinda ita kuma Chelsea za ta kara ne da Burnley.

Kocin Manchester United Louis van Gaal zai dauki bakuncin Swansea a yayinda Southampton za ta ziyarci Liverpool.

Tottenham karkashin sabon kocinta Mauricio Pochettino za ta fafata ne da West Ham, sai kuma West Brom ta kece raini da Sunderland.

Zakarun gasar Championship a kakar wasan da ta wuce watau Leicester za ta fafata ne da Everton sai QPR wacce za ta hadu da Hull.

Arsenal kuwa za ta daukin bakunci Crystal Palace ne a filin Emirates.

Karin bayani