Ba Oboabona a wasan Nigeria/Bosnia

Godfrey Oboabona Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Oboabona na da muhimmanci ga tawagar ta Super Eagles

Dan wasan Nigeria Godfrey Oboabona ba zai buga wasan da kasar za ta buga da Bosnia-Hercegovina a gasar cin kofin duniya ranar Asabar ba saboda rauni.

Dan kwallon mai taka leda a kulob din Rizespor, mai shekaru 23, ya samu rauni ne a zagayen farko na wasan da Nigeria ta tashi canjaras da Iran.

"Sakamakon gwajin da aka yi masa, ya nuna cewa ba zai samu damar taka leda a wasan Bosnia ba," mai magana da yawun tawagar ta Super Eagles Ben Alaiya ya shaida wa BBC.

"Mun yi sa'a cewa bai karye ba, a don haka muna sa ran zai buga wasanmu da Argentina."

Super Eagles - wadanda su ne zakarun Afrika an sa ran cewa za su tsallake zuwa zagaye na biyu tare da Argentina.

Karin bayani