An fitar da Spain daga gasar kofin duniya

An fitar da Spain daga gasar kofin duniya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Spain ta bi sahun Italy wacce aka fitar a irin wannan yanayin a gasar da ta gabata a Afrika ta Kudu

An fitar da masu rike da kanbu Spain daga gasar cin kofin duniya bayan da suka sha kashi a hannun Chile da ci 2-0 a rukunin B.

Wannan shi ne wasa na biyu a jere da aka doke Spain din bayan da Holland ta lallasa ta da ci 5-1 a wasan farko.

Eduardo Vargas ne ya fara zira kwallo a minti na 19.

Sannan kuskuren da mai tsaron gida Iker Casillas ya yi ya baiwa Charles Aranguiz damar zira kwallo ta biyu.

Diego Costa na Spain ya barar da dama mai kyau sannan Sergio Busquets ya sake barar da wata damar a yadi na biyar.

Spain ta bi sahun Faransa da Italy wadanda aka fitar a irin wannan yanayin a Koriya da Japan a 2002 da kuma Afrika ta Kudu a 2010.

Karin bayani