Harin Damaturu da ciwo - Super Eagles

Hakkin mallakar hoto AP

'Yan wasan Nigeria a Brazil sun ce harin da aka kai kan wani gidan kallon gasar cin kofin duniya a birnin Damaturu, inda mutane 21 suka mutu ya sa su kara zage dantse a Brazil.

Jami'in yada labarai na kungiyar Super Eagles, Ben Alaiye ya ce harin abin takaici ne, kuma suna mika ta'aziyyarsu kan wannan rashi da ya ce ya yi wa kungiyar Super Eagles ciwo, don haka za su dage su ci wasansu don wadanda aka kashe.

'Yan wasan sun yi shiru na minti daya don karrama mutanen da harin ya shafa kafin su fara atisaye ana zabga ruwan sama a filin wasa na Campinas da ke birnin Sao Paulo ranar Laraba.

A ranar Talata ne wani bam ya fashe a tsakiyar taron 'yan kallo da ke ganin karawar Brazil da Mexico a birnin Damaturu da ke jihar Yobe.

Najeriya dai za ta yi wasanta na gaba ne a rukunin F da Bosnia a Curutiba a ranar Asabar.