Uruguay ta doke England 2-1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An dade ana zancen Suarez da irin rawar da zai taka

England na cikin hadarin ficewa daga gasar cin kofin duniya bayan da kwallayen biyun da Luis Suarez ya zira suka ba Uruguay damar doke su da ci 2-1.

Suarez ya ci kwallon farko da ka kafin Wayne Rooney ya farkewa England mintina 15 kafin a tashi.

Dan wasan na Liverpool Suarez ya kara kwallo ta biyu mintina shida kafin a tashi, abinda ya sa England ta koma ta karshe a rukunin D.

Rashin nasarar na nufin England za ta fice daga gasar idan wasan da za a yi tsakanin Italy da Costa Rica ya kare a kunnen doki.

Karin bayani