FIFA na binciken nuna wa Kamaru wariya

Hakkin mallakar hoto fifa
Image caption A bara ne Fifa ta kafa wasu tsauraran dokoki masu tsauri game da wariyar launin fata a lokacin wasa

Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta fara daukar matakan ladabtar da Mexico, bayan zargin cewa magoya bayansu sun nuna wariyar launin fata ga Kamaru a gasar cin kofin duniya.

A wata sanarwa da ta fitar, hukumar ta ce an fara binciken ne bayan abin da ta kira halin nuna rashin da'a da magoya bayan 'yan wasan Mexico suka yi.

Wata majiya a hukumar ta shaida wa BBC cewa Fifa na kuma duba kalaman nuna wariyar launin fatar da magoya bayan 'yan wasan Brazil suka yi.

Haka kuma Fifa na binciken batun kwalaye da kuma kyallaye da ke dauke da kalaman wariya da wasu mutane suka daga a karawar Croatia da Rasha.