Kofin Duniya: Suarez ya warke

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Luis Surez na barin asibiti bayan da aka yi masa tiyata a asibiti ranar 22 ga watan Mayu na 2014

Ana sa ran Luis Suarez zai buga wasan Uruguay da Ingila na kofin duniya ranar Alhamis bayan tiyatar da aka yi masa a gwiwa.

kocin Uruguay Oscar Tabarez yana sa ran Suarez zai iya fara wasan amma ya ce ba lalle ya murmure sosai ba.

Shi kuma kyaftin din Uruguay Diego Lugano ba zai yi wasan ba saboda raunin da ya ji a gwiwa, yayin da ake sa ran Jorge Fucile zai maye gurbin Maxi Pereira.

A bangaren Ingila kuwa Alex Oxlade-Chamberlain ya dawo atisaye bayan da ya ji rauni a gwiwa, amma ba tabbas ko zai yi wasan.

Rooney ma dai ba a san ko kocinsu Roy Hodgson zai sa shi ba, bayan da ya buga wasan kofin duniya na tara ba tare da ya jefa kwallo a ragar Italiya ba.